Daga Abdullahi Kebbi
Sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Guangshi Juang, mutum 7 ne aka bada rahoton rasuwarsu, yayin da wasu 4 suka jikkata, sannan wasu 2 Suka bata Bat.
A wani Bangare Kuma gidaje 185 ne suka lalace, yayin da gonaki da dama suka suka Baje.
An tafka asara ta Sama da Dala Miliyan 19.3, haka akwai mutum dubu 9 da suka tsere daga gidajensu, domin neman Tsira da rayuwar su.
Sai dai Gwamnati na ci gaba da rarraba barguna da kayan Tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.