Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka Kamala Hariss zata sanar da bai wa ƙasar Ghana tallafin Dalar Amurka Biliyan 139 a shekara mai zuwa. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
Wannan na zuwa ne dai dai lokacin da Hariss ke ziyara mafi girma a nahiyar Afirka, a ƙoƙarin da Amurka keyi na ƙalubantar tasirin Sin da Rasha na samun karbuwa a nahiyar Afirka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Wasu Mata Na Zanga-Zanga Tsirara Ofishin Jakadancin Amurika
A fiye da shekaru 20 da suka gabata Sin ta zuba jari sosai a nahiyar Afirka, mussamman a bañgaren ababen more rayuwa, haƙar ma’adinai, katako da kuma kamun kifi, yayin da Sojojin haya na Rasha da ake kira Wagner ke bayar da tallafin tsaro a ƙasashe da dama dake nahiyar.
Ziyarar ta Haris wanda ta ƙunshi ƙasashe Tanzaniya, da Zambiya itace ziyarar da wani babban jami’in Amurka ya kai a daidai lokacin da kasar ke ƙoƙarin kyautata alakar ta da nahiyar.
Tun a farkon wannan watan Sakataren gwamnatin ƙasar Amurika Anthony Blinken ya ziyarci kasar Habasha da Nijar, inda ya sanar da bayar da tallafin jin ƙai na Dalar Amurka 150 ga yankin Sahel.
A yau Litinin Hariss zata gana da shugaban Nana Akufo-Addo a Accra, tare da bayar da sanarwar tallafin dalar Amurka 100 domin tallafawa daƙile faɗace -faɗace tare da inganta abubuwa a ƙasashen Benin, Cotedvoure , Ghana da kuma Togo.
A gefe ɗaya ƙasar, Ghana a bara ta gaza biyan mafi yawan bashin da ƙasashen waje ke binta wanda ya kai dala biliyan 29, yayin da kudaden ruwa da hauhawar farashin kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi kuma har yanzu ƙasar na bukatar tattaunawa tare da kamfunan ƙasashen waje masu zaman kansu da kuma masu bayar da lamuni daga kasashen Ketare.
Kasar Sin dai ita ce kasar da tafi kowace ƙasa baiwa Ghana lamuni wanda ya kai kusan dala biliyan 1.9, duk da haka a makon da ya gabata Ma’aikatar kudi ta ƙasar tace tana sa ran samun tabbacin samar da kudaden bayan taron da suka yi a kasar Sin.
A wani labarin kuma, Ayu Ne Ya Jagoranci Rashin Nasarar PDP, Ina Goyan Bayan Dakatar Da Shi — Wike
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce yana goyon bayan dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Idan ba amanta ba, Kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP a gundumar Igyorov na karamar hukumar Gboko a jihar Benue, ya dakatar da Ayu a ranar Lahadi, bayan da aka kada masa kuri’ar yankan kauna kan wasu ayyukan da yayi kuma ake zargin zagon kasa ne ga jam’iyyar ta PDP.