Wata kotu da ke zamanta a unguwar noman salan a Kano ta yankewa wani matashi da ya ke amfani da shafukansa na sohiyal midiya ya ke cin zarafin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, hukuncin zaman gidan kaso na watanni 6 ba tare da zaɓin biyan tara ba, da kuma wasu watanni shida su kuma da zaɓin tara ta naira 50,000.
Matashin mai suna Ɗalha Yusif wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Ƙaraye ne da ke jihar Kano, yayi fice wajen cin zarafi ga jagororin da su ke saɓanin jam’iyyar siyasa, musamman gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Tun da farko dai kotun tana tuhumar Ɗalha Yusif ne da laifin yin rubutu na ɓatanci ga gwamna kano, wanda bisa haka ne shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Ismail Afakallah ya gurfanar dashi a gaban shari’a.
Tuni dai jami’an tsaro su ka ingiza ƙeyar Ɗalha Yusif zuwa gidan yari domin zaman wa’adi.