An bangawa Wasu gungun mutane da ake kyautata zaton cewa, yan fashi da makami ne na POS a kasuwar Afor-Ukwu, dake garin Isiekenesi, na karamar hukumar Ideato ta kudu a jihar Imo.
Lamarin ya faru ne bayan wadanda ake zargin sun yi wa wani Mai shagon POS fashi, sannan suka gudu da injin cire kudi na POS.
Nan take wanda aka yi wa fashin ya kwarmata ihu, wanda ya ja hankalin mazauna yankin wajan kawo mashi dauki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu sulhu tsakanin mu da Yan bindiga, inji Gwamnan Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda ake zargin sun yi kokarin tserewa, kafin kama su.
Kazalika an bayyana cewa, Mutum guda ya mutu cikin wadanda ake zargin, yayin da yan sanda suka dakile fashin na POS a jihar Imo
Bayan kashe mutanen da ake zargi, mutanen yankin sun kai gawarwakin zuwa kasuwar Affor-Ukwu, inda a nan ne aka banka musu wuta.
Sun yi amfani da tayoyi guda uku da man fetur wurin cinna wa gawar-wakin wuta.
Majiyar yajidar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Rundunar yan sandan jihar Imo har yanzu ba ta ce komai ba game da lamarin.