Da Ɗuminsa: Shugaban Sojojin Wagner, Prigozhin ya mutu a hatsarin jirgin sama
Shugaban rukunin Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a ƙasar Rasha.
Hadarin jirgin na kashin kansa ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 10 da ke cikinsa.
KARANTA WANNAN LABARIN:An Bayyana Albashi Da Alawus Na Ministocin Bola Ahmad Tinubu
Rahotanni sun ce wasu da ake zargin sojojin Rasha ne suka harbo jirgin mai zaman kansa a yankin Tver da ke arewacin birnin Moscow.
Kwanan nan, Prigozhin ya yi yunkurin juyin mulki a kan Putin.
Prigozhin ya jagoranci wani boren da bai yi nasara ba kan sojojin Rasha a watan Yuni.
Putin ya bayyana Prigozhin a matsayin “maci amana
A wani labarin kuma:An Bayyana Albashi Da Alawus Na Ministocin Bola Ahmad Tinubu
Birtaniya ta yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai a ofishin jakadancin Burtaniya, Atinuke Akande-Alegbe ya fitar a ranar Laraba, Burtaniya ta yi Allah wadai da tsare Bazoum ba bisa ka’ida ba da sojoji suka yi.