-Inda kuma Dangote, da Bill Gates suka bada tabbacin cigaba da tallafawa jihar.
An bayyana jihar Kano a matsayin wacce ke kan gaba a shirin karfafa kiwon lafiya. Masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa tsakanin su da gwamna Ganduje kan sake duba ayyuka da aka gudanar ta hanyar magana da na’urar zamani (Teleconference) a dakin taro da ake kira Africa House dake gidan Gwamnatin jihar Kano suka bayyana hakan.
Babban sakataren Hukumar kiwon lafiya a matakin farko ta jihar Kano Dr. Tijjani Hussaini yace a ‘yan shekarun nan, shirin kiwon lafiya ya cigaba musamman a matakin farko inda yace an fadada shirin daga matakin riga kafi zuwa kiwon lafiya na iyakan ma’aikatun dake karkashin hukumar kiwon lafiya ta jiha, wanda yayi fatan, nan da shekarar 2021 zai iso ko’ina a jihar kano.
A bayanen da yayi, Dr. Hussainin yace daga Janairu zuwa Yunin shekara ta 2019 ayyukan da shirin ke fuskanta sune samar da kyakkyawan daidaito tsakanin bangaren kiwon lafiya na matakin farko da na biyu wanda ya bada daman kawar da shafin farko.
Ayyukan da ya lissafan sun hada da kiddiddige cibiyoyin bada magani da ake kira (DRF) domin inganta yanayin bin ka’ida wanda har ma an kammala yin hakan a cibiyoyi 132.
Wata nasarar da aka samu itace soma gudanar da shirin hadin kai da dukkan kananan hukumomin jihar guda 44 a tsakanin watan Janairu da Yunin 2019.
An saka mutanen kauyukan a harkar gudanar da shirin domin cimma nasara
Dr. Hussaini yace yanzu haka akwai jadawali kan yadda za’a kara inganta kiwon lafiyar wanda yanzu haka yana jiran kammalawa.
Ya bada tabbacin cewa dukkan bangarorin tattara bayanai kan kyakkyawa shirin basu kalubanci juna ba.
Ya kara da cewa idan ma akwai matsala bata wuce wacce ‘yar kwaskorima kalilan ba.
Dr. Hussaini ya bada tabbacin cewa gwamnatin jiha tana iyaka kokarin ta na inganta dukkan lamura musamman bangaren tara domin yin sabbin tsare-tsare.
Dr. Hussaini yace Jihar Kano bata fuskanci bullan cutar shan inna na daji da ake kira(wild polio virus) ba tun shekarar 2014 daidai wasu cutukan muhalli da Kane kira cVDPV uku kacal aka samu labarin bullarsu a karamar hukumar Tarauni a watan Yuli 2018.
Yace an yi kamfe na wayar da kan jama’a guda 7 na mOPV2 da kuma kamfe daya a fadin jihar a 2018 da dai sauran su.
A jawabin rude taro, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Dangote da Bill Gates kan gudumawar su ga jihar.
Shima a nashi jawabin sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila (Autan Bawo) wanda yayi jawabi a madadin sarakunan jihar ya nuna godiyar su tare da amincewa da irin ayyukan da ake gudanarwa.
Wokilan Hukumar kiwon lafiya matakin farko ta kasa da kuma na AFENET Dr. Adamu Nuhu da Dr. Patrick Mboya Nguku sun nuna farin cikin su kan lamarin.