Babu shakka mu al’ummar jihar Zamfara, muna cike da farin ciki, tun bayan darewar Gwamna Dr. Matawalle, musamman ganin yadda kullum ake samun nasara dangane da abubuwan da suke damun mu a wannan jiha.
Tabbas addu’ar da muka dukufa muna yi ce tasa Allah ya dubi halin da muke ciki ya kawo mana wannan bawan Allah Gwamna Matawalle.
Hakika irin kalaman tsohon Gwamna Abdulaziz Yari abin takaici ne ga al’ummar arewa ma a iya jihar Zamfara ba. Domin ya kamata Gwamna Yari yasan cewa, Gwamnati fa Gaskiya ce, kuma sulhu alkhairi ne.
Mun yi asarar rayuka dukiyoyi da sauran abubuwa da dama a jihar Zamfara, duk ta sanadiyar wadancan rikice-rikece, amma cikin ikon Allah Yanzu komai yana sauka kasa, suna ci gaba da ajiye mukaman su.
Ba za mu so a ci gaba da jib da jini a jihar Zamfara ba, domin wannan jinin Iyayen mu ne da ‘yan uwan mu Musulmi.
Abin takaici ne matuka, yadda Tsohon Gwamna Yari yake fito da hanyoyin bata Gwamnatin Dr. Bello Matawalle a fili. Tun yana yin abin a boye har Allah ya fara nuna mana mu talakawan jihar Zamfara.
A jiye , wani abin damuwa da takaici, an kawo gawar wani mutum gidan Gwamnatin jihar Zamfara, duk da an sa ‘yan jarida su nuna wa duniya cewa sulhun da ake yi a jihar baya iyuwa. Amma sai Allah ya mantad da su cewa kan su suke kara tonawa asiri, suke nuna wa duniya kuma cewa ana ci gaba da samun zaman lafiya kwarai da gaske.
Wato tun bayan hawan Gwamna Dr. Bello Matawalle suke wadannan kulle-kulle. Sun kawo gawar mutum daya don su nuna wa duniya cewa, har Yanzu ana kashe mutane a jihar Zamfara. Amma wani Abin godiyar Allah, shine, tabbas an samu saumi in dai har mutum guda za a dauko a kawo gawarsa gidan Gwamnati. Wanda a baya Allah kadai yasan mutanen da ake kashewa a kowacce safiya.
Kuma shin me yasa lokacin Gwamna Yari ba a taba kawo wa ko da gawar sauro gidan Gwamnatin jihar Zamfara ba?
Kar Gwamna Yari ya manta cewa, wannan sulhu da mai girma Gwamna Matawalle yake yi, wallahi ko iya Yanzu haka ya zamo mana alkhairi a jihar Zamfara.
Domin in mai karatu zai duba cikin wannan hotuna da suke biye, yasan cewa wallahi al’ummar jihar Zamfara sun sha wahala matuka a baya, domin hotuna ne da suke dauke da irin kisan gillar da akai wa al’ummar jihar Zamfara a wancan lokacin, kafin zuwan Gwamna mai sulhu wato Gwamna Matawalle.