Watanni biyu bayan Roman Abramovich ya yi murabus daga mallakar Chelsea, Todd Boehly, hamshakin attajirin nan dan kasar Amurka, an tabbatar da shi a matsayin sabon mamanlakin kungiyar.
Abramovich ya sauka ne makonni bayan da kasarsa ta haihuwa, Rasha ta fara mamaye Ukraine.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo, babbar kungiyar ta Premier ta tabbatar da cewa an amince da yarjejeniyar Boehly don siyan kulob din na yammacin London.
“Kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea na iya tabbatar da cewa an amince da sharuɗɗan sabon rukunin mallakar, wanda Todd Boehly, Clearlake Capital, Mark Walter da Hansjoerg Wyss ke jagoranta, don samun ƙungiyar.”
“Daga cikin jimillar jarin da ake yi, za a yi amfani da fam biliyan 2.5 don siyar da hannun jarin da ke cikin Kulub din kuma za a saka irin wadannan kudaden a cikin asusun ajiyar banki na Burtaniya da aka daskarar da niyyar bayar da gudummawar dari bisa dari 100% ga ayyukan agaji kamar yadda Roman Abramovich ya tabbatar.
“Za a buƙaci amincewar gwamnatin Burtaniya don fitar da kudaden daga asusun ajiyar bankin Ambromavic dake Burtaniya da aka daskarar.
“Bugu da kari, sabbin masu hannun jarin za su kashe £1.75bn wajen kara zuba jari domin amfanin kungiyar. Wannan ya haɗa da saka hannun jari a Stamford Bridge, a Bangaren matasan Yan wasa, Ƙungiyar Mata, Kingsmeadow da ci gaba da ba da tallafi ga Gidauniyar Chelsea.
“Ana sa ran kammala siyar da kungiyar a ƙarshen Mayu bisa ga duk takaddun da suka dace. Za a bayar da ƙarin cikakkun bayanai a nan gaba ” kamar yadda kungiyar ta sanar.