An cafke wani ɗalibi ɗan Najeriya mai safarar hodar iblis, a Panchkula, birnin Haryana, na ƙasar Indiya.
Ɗalibin mai suna Nwosu Echezoma wanda akafi sani da Amaica, mai shekara 29 a duniya, ya shiga hannun hukuma ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairun 2023. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Baturiya ta biyo mijinta baƙar fata sun dawo Afrika da zama, sun rungumi noma hannu bibbiyu
An kuma ƙwace hodar iblis mai nauyin kilogiram 15.56 daga hannun wanda ake zargin, wanda yake karatun digirin sa a fannin haɗa magunguna a wata makaranta a Mullana, birnin Ambala na ƙasar, a cewar ƴan sanda.
An cafke shi bayan samun bayanai daga hannun wani mai suna Surajpal Singh wanda akafi sani da Robin, mai shekara 34 a duniya, wanda aka cafke ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 8.78 a ranar 9 ga watan Fabrairun 2023.
Bayan ƴan sanda sun tsare Singh na tsawon kwana biyu, inda a lokacin ne da ake tuhumar sa ya bayyana wajen wanda yake samun ƙwayoyin, hakan ya sanya aka cafke Nwosu.
“Ɗan Najeriyan yana samo ƙwayoyin sa daga birnin Delhi sannan ya rarraba su a tsakanin ciki da wajen Ambala. Wata kotu ta ba ƴan sanda umurnin tsare shi na tsawon kwana biyu. Za a cigaba da bincikar sa domin gano abokan harƙallar sa.” A cewar ƴan sanda.
Buhari Ya Bukaci UAE Ta Janye Takunkumin Da Ta Sanya wa Najeriya
A wani labarin na daban kuma shugaba Buhari ya nemi ƙasar Larabawa da ta cire takunkumin da ta ƙaƙabawa ƴan Najeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dage takunkumin da gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanya wa ‘yan Najeriya kan dokar hana biza.
A wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa ya fitar a ranar Talata, Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan