Wata baturiya wacce ta auri wani ɗan Afrika ta bayyana yadda su duka suka baro Amurka suka dawo Afrika da zama domin tara kuɗaɗe.
Baturiyar ta bayyana cewa sun gina gidansu ne a ƙasar Kenya da kuɗin su. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Ƙarancin kuɗi: Yadda ƴan Najeriya suka koma bani gishiri in baka manda
Gidan na su yana a cikin wani ƙatoton fili wanda suke amfani da shi wajen yin harkokin kasuwancin su na noma.
A cikin bidiyon wanda ta sanya a TikTok ya nuna irin girman da gonar su take da shi inda aka haɗa da kiwon dabbobi da noman kayan abinci.
Mutane da dama waɗanda suka tofa albarkacin bakin su akan bidiyon baturiyar, sun bayyana cewa mutane da dama basu da masaniya kan tarin arziƙin da nahiryar Afrika take da shi ba.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
Imad Jeroua ya rubuta:
“Mutane kaɗan ne kawai suka san cewa a Afrika idan mutum ya rasa aikin sa, zaka iya riƙe gidanka, wayat salula da mota,, babu basussuka a can.”
AKINYI ya rubuta:
“Kada ki gaya musu, za su zo su cika mana nahiya. Wasu abubuwan gwara an yi shiru ba a gayawa duniya su ba.”
Ɗan Najeriya Yayi Wuff Da Kyakkyawar Budurwa Ƴar Indiya, Bidiyon Bikin Ya Ƙayatar
A wani labarin na daban kuma, wani ɗan Najeriya ya lallaɓa ya aure wata ƴar ƙasar Indiya.
Wani bidiyon bikin wani ɗan Najeriya da masoyiyar sa ƴar ƙasar Indiya ya bazu a shafin sada zumunta na TikTok.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @grakeshots a TikTok ya sanya, mutane da dama sun kalle yayin da suke taya masoyan biyu murna.