Wata Kotun Majestire dake Fada a Zaria ta Jihar Kaduna ta garkame wata mallamar Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya mai suna Ebong Joy da kuma Ƴar ta inda za su yi zaman gidan yari na wata shida da kuma shekara bakwai sakamakon samun su da karyar cewa an yi garkuwa da su.
An samu Akpan da yar ta mai suna Inyene Akpan dake ajin karshe a jami’ar da laifin zamba cikin aminci tare da yunkurin karkatar da hankalin jama’a zuwa labarin Ƙarya, kamar yadda Alkalin Kotun Chif Majestire Abdullahi G. Maigamo ya yi hukunci.
Kamar yadda wata takardar kotu ta fitar, Mis Akpan da diyar tata Inyene Akpan sun yi karyar cewa an yi garkuwa da su ne inda suka dora alhakin hakan kuma kan wasu yan kungiyar Manyan Malaman Jami’o’i ta Kasa wato SSANU reshen Jami’ar ABU.
Cikin wadanda take zargin Akwai Muhammad Gimba Alfa da Muhammad Inusa da Lawal Yakubu Hunkuyi da Haruna Mohammed da Salisu Isa gani da Rabaran J.F Bukka dukkanin su malamai a Jami’ar ABU.
Bayan dai da aka tsananta bincike ne daga ɓangaren kotu, Alkalin Kotun Chif Majestire Maigamo ta same matar da diyar da Laifuka uku.