An fitar da rukunan gasar share fage ta gwamna Victor Okezie Ikpeazu wato gasar share fage ta 2020 donin ƙungiyoyoyin ƙwallon ƙafa su shirya don tunkarar sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 wato sabuwar kakar wasa ta NPFL.
An fitar da jerin rukunai guda uku wato rukunin A da rukunin B da kuma rukunin C. Ga yadda aka fitar da rukunan kamar haka:
Rukunin A:
Enyimba.
Kwara United.
Heartland.
Rivers United.
Rukunin B:
Enugu Rangers.
Akwa United.
Abia Comets.
Plateau United.
Rukunin C:
Mountain Of Fire.
Abia Warriors.
F/C Ifeanyi Uba.
Dakkada F/C.
Za a kwashe kwanaki ana fafata wannan gasar ta share fage da manayan ƙungiyoyoyin ƙwallon ƙafa zasu gwada ƙwanjinsu.