Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a safiyar ranar Litinin din nan ta ce an gano dalibin da ya bace dan aji 200 na Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta, Solomon Destiny, kuma yanzu haka yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya aikewa manema labarai.
An bayyana ceaa, “Na gode, mambobi masu girma, na manema labarai, ayyukanku sun bayar da sakamako mai kyau ga jama’a.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa an gano dalibinmu da ke aji na 200 kuma yana raye amma a halin yanzu yana karbar magani.”
KARANTA WANNAN KKK Chelsea Sun Gano Matsalarsu
Idan dai za a iya tunawa, shugabannin kungiyar daliban jami’ar sun koka da cewa an ga Solomon a kauyen Ogboja da ke kusa da Oluwo-Osiele a Abeokuta kuma an nemi bayanai masu kyau da za su taimaka wajen gano shi.
A halin da ake ciki, shugaban sashin hulda da jama’a na FUNAAB, Mista Kola Adepoju yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ya ce “Eh, dalibin mu ya bace kuma Hukumar Jami’ar mu ta tashi tsaye ta hanyar kai rahoto ga hukumomin tsaron da abin ya shafa.
“Muna so mu tabbatar wa iyaye ko masu kula da dalibin mu da ya bace, da abokan aikinsa da sauran jama’a, cewa jami’an tsaro na yin duk abin da ya dace don gano shi tare da dawo da shi ga iyayensa da abokan aikinsa lafiya. ”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Adepoju yayin da yake tabbatar da wannan labarin na farin ciki ga wakilinmu ya ce “Bayanan da muke da su yanzu sun yi kadan. Zan yi muku cikakken bayani daga baya. Na gode.”
A Wani Labarin Kuma DSS Ta Bankado Zanga-Zangar Da Wasu ‘Yan Siyasa Ke Shiryawa FG
Hukumar tsaron farin Kaya ta kasa a ranar Litinin din nan ta ce ta bankado shirye-shiryen da wasu ‘yan siyasa ke yi a fadin kasar nan na gudanar da zanga-zanga don bata sunan gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro kan al’amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki.
DSS ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dr Peter Afunanya ya fitar.