Gwamnatin tarayya ta roki shugabannin kungiyar kwadago ta Kasa da su janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka shirya farawa ranar Talata.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ne ya yi wannan roko a ranar Litinin din nan a Abuja.
Ya bayyana hakan a matsayjn koma bayan nasarorin da gwamnatin tarayya ta samu, da dai sauransu a matsayin dalilin rokon yayin da ya yi alkawarin halartar duk wani abu da kungiyar ta NLC ta shirya gabatarwa, idan aka ba su lokaci don sasantawa.
KARANTA WANNAN NLC, TUC Sun Shiga Ganawa Da Wakilan Gwamnatin Tarayya
Lalong ya ce, “Ya zama wajibi a yi kira ga shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da su dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu, domin irin wannan mataki zai yi illa ga nasarorin da aka samu da aiki ga ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa baki daya.
“Bugu da kari kuma, zan bukaci shugabancin kungiyar kwadago ta Kasa ta su ba wa wannan gwamnati wani lokaci don warware matsalolin da ke faruwa a kasa baki daya.
“Ya kamata a gane cewa ba da dadewa ba ne maigirma shugaban kasa ya rantsar da majalisar ministocin wannan gwamnati, kuma dukkan ‘yan majalisar ministocin suna kokari wajen karbar bayanai daga MDAs dinsu.
“Saboda haka batutuwan da shugabannin kungiyar NLC suka kawo wasu batutuwa ne da ni da Karamin Ministan Kwadagobda aiyuka za mu yi bayani nan da ‘yan makonni masu zuwa, muna da niyyar magance su gaba ɗaya.
“Saboda haka, na yi amfani da wannan dama don tabbatar wa ma’aikatan Najeriya cewa wannan gwamnati ba za ta taba daukar su da wasa ba, ko kuma ta kasa yaba goyon bayansu da fahimtarsu.
Za mu ci gaba da bin manufofin da ke samar da ɗimbin ayyukan yi a kowane fanni na tattalin arziki tare da duba ƙalubalen da suka fito daga manufofin gwamnati. Ba za mu iya yin hakan ba a cikin yanayin da babu zaman lafiya a masana’antu,” in ji shi.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa A halin da ake ciki, Ministan ya bayyana cewa, duk da cewa har yanzu ma’aikatar ba ta samu sanarwar shirin yajin aikin kamar yadda doka ta tanada daga kungiyar NLC ba, ma’aikatar za ta yi taro da shugabannin kwadago da karfe uku na ranaa ranar Litinin din nan da nufin dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa.
A Wani Labarin Kuma An Gano Wani Dalibin Ajin 200 Na Jami’ar FUNAAB Da Ya Bata
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a safiyar ranar Litinin din nan ta ce an gano dalibin da ya bace dan aji 200 na Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Abeokuta, Solomon Destiny, kuma yanzu haka yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya aikewa manema labarai.