Hukumar EFCC reshen Jahar Kaduna tayi nasarar cafke wani matashi mai suna Aliyu Iliyasu bisa laifin cin amana, inda hukumar ta gurfananar dashi a gaban mai Shari’a M. T. Tukur, a wata babban Kotu dake Kaduna. Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
An fara tuhumarsa kamar haka inda akace ” Kai Aliyu, a watan rana cikin watan Disamba na shekarar 2019, Kotu na tuhumarka akan zunzurutun kudade kimanin miliyan shida da dubu dari bakwai da saba’in da biyar (#6775000.00), inda Abubakar Sarki ya baka domin ka saya masa mota kirar Mercedes Benz GLK SUV, inda kaci amana akan hakan, wanda wannan yayi dai-dai da laifin cikin kundin Shari’a na Kotun Panel na sashi 296 na shekarar 2017, a Kaduna. Wanda hakan nada hukunci a sashi na 297 a kundin Shari’a Kotun Panel.
KARANTA:- Gwamnonin PDP sun ce ba wanda ya isa kawar da matsalar Najeriya idan ba PDP ba
Amma sai dai bai amince da tuhumarsa da akeyi ba, sai dai alkali mai kare Kotu Jamil Musa, ya roki kotun data sanya rana da za’a fara gudanar da wannan Kara. Sannan shi kuma Alkali mai kare Aliyu Iliyasu ya bukaci kotu data bashi beli.
Mai shari’a Tukur, ya baima Aliyu Iliyasu beli akan naira miliyan daya, tare da gabatar da shaidu kwarara guda uku.
Sai dai matsalar ta dawo sabuwa, inda Abubakar Sarki ya tura karar ga hukumar ta EFCC, inda yace a wata rana cikin watan Disamba na shekarar 2019, ya baiwa Aliyu Iliyasu kudi naira miliyan shida da digo bakwai kan ya saya masa mota, amman sai ya kawo masa wadda ba ita suka shirya ba.
Shidai Abubakar Sarki a lokacin bai karbi motar ba, inda Aliyu Iliyasu yayi masa alkawarin dawo masa da kudaden sa baki daya.
Sai dai Aliyu Iliyasu ya dawo masa da naira miliyan biyu ne kacal, inda Abubakar Sarki yana ta masa magana kan ya cika masa sauran kudaden amma abun yaci tura.