A jiya ne aka gurfanar da wani direban mota mai shekaru 49, Mai suna Mr Olalekan Adedeji a gaban Kotun Majistare ta Jihar Osun, da ke zaune a Ilesha, bisa zargin sa da sanadiyar mutuwar fasinjoji shida.
An tuhume shi da laifuka shida, da ka iya haddasa hatsari, Wanda ya hadar da tukin mota ba tare da takardun hanya ba, da dai sauran su.
Dan sanda mai gabatar da kara Insfecta Jacob Akintunde ya bayyana wa kotun cewa “A ranar 17 ga watan Yuli, da misalin karfe 6:45 na yamma, a kan babbar hanyar Ilesha zuwa Ife na jihar Osun, ka tuka motar kirar Yotang Luxurious cikin gagganci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji 6, a cikin wata mota kirar Toyota Hiace. sannan kuma hakan yasa motocin sun talalace, da darajarsu ta kai N29million. ” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kashe yan bindiga 4 a Osun
Ya ce Adedeji yayi tuki akan babbar hanyar ba tare da takardar shaidar inshora ba, don kare kimar aikin shi.
“Laifin ya saba da hukunci a karkashin sashe na 139, 142, da 548 na dokokin RTA na dokar tuki a Nigeria na shekarar 2015.”
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Kazalika Lauyan Wanda ake zargin V. C. Dadi, ya roki kotun da ta bada belin din matukin motar.
Sai dai Kuma daga bisani Alkalin kotun mai shari’a Misis Modupe Awodele ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi naira miliyan biyar, tare da mutum biyu masu tsaya masa.
inda kuma ta dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Satumba shekarar 2021.
Comments 1