Wata mata mai ƴaƴa biyar cikin takaici ta bayyana wani abin baƙin ciki da ya taɓa faruwa da ita, wanda yayarta da mijinta suka yi mata.
Mata mai suna Ange tace bata samun kwanciyar hankali ba a rayuwata sannan yayarta itace silar faɗawarta cikin matsaloli. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Hukumar ICPC ta cafke wata budurwa mai siyar da sababbin takardun kuɗin naira
“Lokacin da nake ƙaramar yarinya, tana takuramin ta hanyar cika min aikace-aikace kamar wata ƴar aiki. Bata bari nayi karatu ba ta hanyar lafkenu da aikin gida. Dole na fita makaranta na dawo ina kula da ƴaƴanta.”
Ta tuno wata rana lokacin da bata da lafiya wacce ta sanya aka kwantar da ita har na tsawon wata biyu a asibiti.
A wannan lokacin cikin mijinta da yayarta babu wanda ya zo asibiti ya duba ta ko da sau ɗaya ne. Hakan ba ƙaramin ciwo yayi mata ba.
“Bayan na dawo gida daga asibiti, na kaɗu matuƙa bayan na gano cewa mijins ya ƙyale ƴaƴanmu ya koma rayuwa tare da yayata. Naji takaici sosai. Duk idan na kira shi a waya, sai ya ƙi ɗauka.” A cewar ta.
Domin tabbatar da zargin da Ange take yi, sai ta ɗauki ƴarta suka tafi gidan yayarta domin ganewa idon su.
“Lokacin da muka shiga falon kawai sai muka tarar suna ta raƙashewa, suna shan barasa suna jindaɗin su kawai.”
Ange daga nan sai ta dawo gida bayan sun gama faɗan da za suyi tare da fatan cewa mijinta zai biyo su, amma sai ya ƙi.
An Gurfanar Da Wani Magidanci Gaban Kotu Saboda Ya Ƙaro Aure
A wani labarin na daban kuma, an gurfanar da wani magidanci gaban kotu saboda ya ƙaro aure.
Ƴan sanda a ranar Laraba sun gurfanar da wani mutum mai suna Edmund Uzoma, a gaban kotun majistare dake Yaba, jihar Legas, bisa zargin ya ƙara aure.
An gurfanar Uzoma a gaban majistare Adeola Olatunbosun bisa tuhomomi guda uku na ƙara auren mace ta biyu da bayar da bayanan ƙarya a jikin katin shaidar aure.