By Abbas Yakubu Yaura
An gurfanar da wani magidanci mai shekaru 44 a duniya, mai suna Onyekwere Ezewonye, a jihar Legas, bisa zarginsa da laifin lakada wa ‘yar uwarsa dukan kawo uka.
Wanda ake tuhumar dai ya bayyana a gaban wata kotun Majistare dake Ojo a kan tuhume-tuhume guda biyu na cin zarafi da kuma lalata dukiya da gangan.
Sai dai ya musanta tuhumar da ake masa a gaban alkalin kotun, Mista Ademola Adesanya.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Simeon Uche, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Disamba a wani wuri mai tazarar Kilomita 23, kusa da babban titin Legas-Badagry.
Uche yace wanda ake tuhumar ya lakada wa mai karar, Happiness Igwe dukan tsiya, biyo bayan rashin fahimtar da suka yi kan sayar da kadarorin iyalansu.
A cewar dan sanda mai gabatar da kara, wanda ake kara ya afkawa Igwe, wanda ya kalubalance shi da sayar da kadarar.
Sannan ya kara da cewa wanda ake kara, a wannan ranar, da gangan ya lalata rufin wani bungalow mallakar wata Misis Stella Eze.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Uche ya bayyana cewa laifukan sun ci karo da sashe na 168 da 350 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Kazalika Kotun ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa, sannan ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairu.