An gurfanar da wasu mutane biyu da laifin satar bututun iskar gas a Legas
Rundunar ‘yan sanda a Legas ta gurfanar da wasu mutane biyu, Ifeanyi Chukwu da Amadi Orji a gaban wata kotun Majistare ta Ojo da ke Legas, bisa zargin su da satar iskar gas.
Chukwu, mai shekaru 42 da Orji, mai shekaru 50, sun gurfana a gaban kotun Majistare, Mista LK J Layeni, kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi hada baki da sata.
KARANTA WANNAN LABARIN:APC ta caccaki Gwamnan Rivers kan gabatar da kasafin kudi ga ƴan majalisa hudu
Sai dai sun musanta zargin da ake musu.
Tun da farko dai mai gabatar da kara, Dokta Simon Uche ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a watan Disambar 2022, a sashen Fancy and Furniture na kasuwar kasa da kasa ta Alaba da ke Ojo, Legas.
Ya kara da cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne wajen satar iskar gas mallakin wani Victor Nzekwe, inda ya kara da cewa kudin silinda din ya kai Naira miliyan 20.
A cewarsa, daga karshe ‘yan sanda sun cafke wadanda ake tuhuma tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Laifin a cewarsa ya sabawa tanadin sashe na 287 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas na shekarar 2015.
Don haka Alkalin kotun ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi Naira miliyan daya kowanne tare da masu tsaya masa guda biyu kowanne a daidai adadin sannan kuma ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2024, domin ambatonsa.
A wani labarin kuma:Kotu ta ɗaure mutumin da ya amsa laifin satar mota
Wata Kotun Majistare ta Badagry da ke Legas, a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai shekaru 52, Charles Ogaba saboda ya amsa laifin satar mota.
Alkalin kotun, Fadahunsi Adefioye ya bayar da umarnin tsare Ogaba bayan ya amsa laifuka biyu da suka hada da sata da canza fasalin ta.