Mata da maza na cikin hawaye a yankin Adankolo na jihar Kogi bayan wasu mutane sanye da kakin jami’an tsaro sun kashe mutum uku a garin.
Yayin da tawagar BBC Pidgin ta isa wurin ta tarar da daya daga cikin wadanda suka rasa ransu ana yunkurin binne shi.
Maza da mata na cikin alhini a garin da a da yake cike da hada-hada.