Ana zargin mai horas da kulob ɗin Nantes, Antoine Kombouare, da ajiye ɗaya daha cinin ƴan wasan sa bayan ya ƙi yadda ya karya azumin sa ranar wasa.
Kocin ɗan ƙasar Faransa ya ƙi ɗaukar ɗan wasan baya Jaouen Hadjam, a cinin ƴan tawagar sa a shan kashin da kulob ɗin yayi da ci uku sa nema (3-0) a hannun Reims a ƙarshen makon nan. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Garin neman gira: Budurwa ta mutu wajen ƙara mata girman mazaunanta
Ɗan wasan mai shekara 20 a duniya ya buga wasanni tara tun bayan da ya zo kulob ɗin daga Paris FC a watan Janairu.
Hadjam ya ƙi yarda ya karya azumin sa a ranar wasan saboda hakan ya saɓawa addini.
Sai dai, Kombouare, ya haƙiƙance cewa ba hukunta ɗan wasan yayi ba, yayi hakan ne domin ya kare shi daga samun rauni.
A kalamansa:
“Jaouen? Babu wata rigima. Zaɓin sa kuma na mutunta shi. Wannan ba hukunci bane amma ina da tsari.”
“A cikin ranakun sati babu wata matsala da ƴan wasa masu azumi. A shirye nake na goya musu baya idan akwai buƙatar hakan. Mun san cewa ba lokaci bane mai sauƙi.”
‘Amma a ranar wasa kada kayi azumi. Sannan waɗanda suke azumi ba zan sanya su cikin ƴan tawaga ba. Bana son su samu rauni.
Barcelona Ta Bayyana Gaskiya Dangane Da Yiwuwar Dawowar Messi Kulob Din
Mataimakin shugaban kulob ɗin FC Barcelona, Rafa Yuste, ya tabbatar da cewa kulob ɗin ya tuntuɓi Lionel Messi domin duba yiwuwar dawowar sa kulob ɗin.
Ɗan wasan na ƙasar Argentina ya bar Barcelona cikin ƙwalla a shekarar 2021. Daga nan ya koma Paris Saint Germain a kyauta inda ya sanya hannu akan kwantiragin shekara biyu wacce zata ƙare a ranar 30 ga watan Yunin 2023.