An jefi Tinubu da wasu Kalamai masu ɗaci kan ziyartar Obasanjo
An yi wa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu Dariya da ba’a a kan ziyarar daya kai wa Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo.
Tinubu ya gana da Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, jihar Ogun a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar PDP Ce Ke Rura Wutar Rikicin Ganin An Tsige Abdullahi Adamu—- APC
An yi imanin ganawar da shugabannin siyasar yankin Kudu maso Yamma shawara ce a tsakanin su.
Da yake mayar da martani, Deji Adeyanju, wani mai fafutukar kare haƙƙin bil adama a Abuja, ya ce ziyarar da Tinubu ya kai wa Obasanjo ya nuna cewa siyasa wani abu ne daban.
Adeyanju ya tuna yadda ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya taba kiran Obasanjo da mai Maguɗin zaɓe.
Ya kuma bayyana yadda Tinubu ya roki ƴan Najeriya da kada su dauki Obasanjo da muhimmanci kan sukar Shugaba Muhammadu Buhari a Shekarar 2019.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Adeyanju ya bukaci ƴan Najeriya da su guji fada da kansu kan ƴan siyasa.
A cewar Adeyanju: “Tinubu wanda ya kira Obasanjo mai magudin zabe wanda bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba a lokacin da ya caccaki Buhari a 2019 a yau ya kwashe sa’o’i tare da tuntubar Obasanjo, Siyasa wani abu ne daban.
“Kada ku yi fada da juna kan ‘yan siyasa. Ba su da daraja. Na san su sosai.
“Dukkan su abokai ne na kut da kut da abokan kasuwanci. Jeka ka yi sauri don ka gaya musu a fuskoki. Babu abin da suka tsana fiye da haka.”