Jam’iyyar APC ta ce ‘yan adawar na rura wutar rahotannin shirin tsige shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu.
Sakataren yada labaran Jam’iyar na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Morka ya ce wannan ikirarin ya samo asali ne daga tunanin masu daukar nauyin rura wutar rikicin “da alama ba su damu da gagarumin nasarorin da Adamu ya samu ba” tun lokacin da ya hau karagar jagorancin APC.
Kakakin ya bayyana cewa jam’iyyar da shugabannin ta sun mayar da hankali ne wajen gina Kwamitin yakin ne man zabe mai karfi, kuma ba za su shagaltu da kururuwar masu yada jita-jitan banza ba.
Morka ya zargi jam’iyyar PDP da “Kitsa makirci a APC maimakon mayar da hankali kan gyara rikicin cikin gidanta da ya yi kamari”.
Jam’iyyar ta kara da cewa kwamitin zartaswarta na kasa ya kasance a dunkule a karkashin jagorancin Adamu “tare da sadaukar da kai ga dukkannin hanyoyin da za su kawo nasarar lashe zabe mai zuwa”.