Kungiyar CBJ a yau Lahadi ta bayyana gamsuwarta bisa yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya baki domin ganin an kawo karshen rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Jukun da Tibi a jihar Taraba.
Anule Emmanuel, shugaban kungiyar, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga menama labarai a birnin tarayya Abuja.
Anule ya ce kungiyarsu ta ji dadin yadda shugaba Muhammadu Buhari ya nuna halin dattako wajen ganin ya kawo karshen rikicin da ke tsakanin kabilun biyu, wanda aka jima ana fafatawa a tsakani.
Kungiyar CBJ kungiya ce ta kwararrun masu kafafen watsa labarai ‘yan asalin jihar Binuwe wanda suke da membobi a fadin kasarnan.