An kaddamar da dalar shinkafa mai kunshe da buhunan paddy miliyan daya a Abuja.
Dalar gyada, wadanda su ne irinsu na farko a Nahiyar, a karkashin shirin Babban Bankin Najeriya na Anchor Borrowers .
Babban bankin ne ya hada buhunan shinkafar, daga manoman da suka ci gajiyar shirin a matsayin biyan basussukan da suka karba maimakon kudi.
Za a sayar da su ne ga masu sarrafa shinkafa a farashi mai rahusa a wani abin da CBN ya bayyana a matsayin kokarin daidaita farashin kayan.
A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce kaddamar da buhunan shinkafa miliyan daya, na dalar shinkafa, ya nuna cewa kasar na cigaba da samun wadatuwa a fannin samar da abinci.
Shugaban, a wajen kaddamar da dalar a Abuja, ya shawarci kungiyoyin noma, da har yanzu ba su shiga cikin shirin Anchor Borrowers ba da su yi hakan domin tallafa wa manufar wadatar abinci a kasar.
Ya yi farin ciki da hada-hadar kamfanonin shinkafa na kasar daga goma sha biyar zuwa sama da hamsin kuma yana da tabbacin za a kara samar da guraben ayyukan yi idan karin guda biyu a Legas da Katsina suka fara aiki.
Shugaban, ya yaba da kokarin da babban bankin kasar ke yi na farfado da kasuwar hada-hadar kayayyaki ta kasar bayan amincewarsa kuma yana fatan hakan zai haifar da samar da masu sayan amfanin gonakin noma, ta yadda za a kawar da noma zuwa kasuwar hada-hadar kudi.