Wani harin bam a birnin Mazar-i-Sharif na Arewacin ƙasar Afghanistan a ranar Asabar, ya halaka wani jami’an tsaro sannan ya jikkata wasu ƴan jarida da ƙananan yara da dama, a cewar ƴan sanda da shaidun gani da ido.
Harin na zuwa ne kwana biyu bayan wani mai harin ƙunar baƙin wake, ya halaka gwamnan Taliban a gundumar Balkh ta Arewa. Ƙungiyar IS itace ta ɗauki nauyin harin. Rahoton jaridar Punch
KU KARANTA KUMA: Shawarar Pauline Tallen Kan Mata Masu Juna Biyu Da Ake Kora Daga Makarantu
Harin da aka kai wa Mohammad Muzammil, a birnin Mazar-i-Sharif ranar Alhamis, shine lokacin farko da aka halaka wani babban jami’in Taliban tun lokacin da suka dawo kan mulki a shekarar 2021.
Harin na ranar Asabar, ya auku ne yayin wani biki na karrama ƴan jarida a Afghanistan a wani wajen taron a birnin Mazar-i-Sharif. Ƴan sanda sun bayyana cewa wani mai gadi ya rasa ransa sannan wasu ƴan jarida biyar sun samu raunika.
“Naji wata ƙara mai ƙarfi…nan da nan sai wajen ya hargitse yayin da mutane suke ƙoƙarin samun hanyar tserewa.” A cewar wani ɗan jarida Atif Arian da ya samu rauni.
“Wasu ƴan jarida sun samu raunika sosai.”
Kakakin ƴan sandan Balkh, Mohammad Asif Waziri, yace wasu ƙananan yara uku suna daga cikin waɗanda suka samu raunika.
Arian yace bam ɗin ya fashe ne lokacin da wasu yara suke rera taken ƙasar bayan wani jami’in Taliban yayi jawabi a wajen.