Wata babbar kotun tarayya da ke Bauchi ta yanke wa wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP biyu a jihar Bauchi, Aminu Umar Gadiya da Saleh Hussaini Gamawa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, bisa samun su da laifin hada baki da kuma karkatar da makudan kudaden haram Naira N142, 460,000.00.
Mai shari’a Hassan Dikko ya yankewa Gamawa da Gadiya hukunci ne a ranar 2 ga watan Maris, yayin da yake yanke hukunci kan tuhume-tuhume 2 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shigar a kan wadanda ake kara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Barau Jibrin Ya Bukaci Masoyansa Suyi APC Sak
Shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a na INEC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar.
An fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2018 sannan kuma a ranar 16 ga Oktobar shekarar 2018 aka sake gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na zargin karbar sama da Naira miliyan 142 don yin tasiri a sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2015 a jihar Bauchi.
Hukunce-hukuncen zaman gidan yarin kan yan biyun za su gudana a lokaci guda daga ranar 2 ga watan Maris, 2023.
Wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi, inda suka kafa hanyar da za a ci gaba da shari’ar.
Sai dai a karshen shaidar an gabatar da adireshi na karshe a rubuce, an yi musayarsu tare da karbar su a ranar 17 ga watan Janairun wannan shekara, inda masu gabatar da kara suka bukaci kotu da ta hukunta wadanda ake tuhuma kamar yadda ake tuhumar su.
Mai shari’a Dikko, ya yanke hukuncin a ranar 2 ga watan Maris, 2023.
A wani labarin kuma, Shawarar Pauline Tallen Kan Mata Masu Juna Biyu Da Ake Kora Daga Makarantu
Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta shawarci minista mai jiran gado ta ma’aikatar da kada ta bari a ci gaba da korar ‘yan mata masu ciki daga makaranta.
A cewarta, ilimi shine mabuɗin karfafawa ‘yan mata gwiwa, domin su samu ci gaba ta kowace fuska.