Wani mutum mai suna Jamilu Muazu a ranar Litinin ya bayyana a gaban wata babbar kotun majistare ta Wuse Zone 6 a Birnin Tarayya Abuja, bisa zarginsa da damfarar abokin sana’arsa har naira miliyan 12.
Lauyan mai gabatar da kara, Peter Ejike ya shaidawa kotun cewa an kawo karar ne a a ofishinsu dake AIG Zone 7, domin bincike a ranar 23 ga watan Fabrairu.
Lauyan da ya shigar da karar ya ce wanda ake kara ya damfari wanda ya shigar da karar, Aliyu Musa domin ya shiga harkar kasuwanci ta saye da sayarwa na shinkafa tare da shi.
Ya kara da cewa wanda ya shigar da karar, ya tura naira miliyan 12 a cikin asusun bankin wanda ake tuhuma.
Ya ce bayan ya tura masa kudin cikin asusun wanda ake tuhuma, kawai sai ya sauya manufar tura masa kudin ya zama na shi daga bisani ya tsere.
Lauyan masu gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashi na 312 da 322 na dokar manyan laifuka.
Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Alkalin Kotun Mai shari’a Umar Dodo ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N200, 000 tare da mutum biyu masu tsaya masa, wanda dole ne su kasance ma’aikatan gwamnati a kowane mataki.
Ya daga sauraron karar har zuwa 14 ga watan Satumba domin sauraron ta.