By Abbas Yakubu Yaura
An kama wani matashi dan shekara 35 mai suna Jude Nduka bisa zargin yi wa wasu ’yan mata biyu ‘yan uwan juna fyade a hanyar Okpanam ta jihar Delta.sannan ana kuma zargi wanda ake zargin da yiwa daya daga cikin ‘yan matan ciki ciki.
Rahotannin sun bayyana cewa kama shin ya biyo bayan korafin da uwar ‘yan matan biyu ta kai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Mohammed Ari, inda ya yi cikakken bayanin ga kwamandan Eagle-Net Squad daya bi wanda ake zargin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Edafe Bright, a wata sanarwa daya fitar a ranar Asabar, yace rundunar ‘yan sandan ta musamman ta kama wanda ake zargin bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan.Bright ya bayyana cewa wanda ake zargin yana zaune a gida mai lamba 10 Obi Onuwe Street, bayan Kowen Plaza, Asaba, ya yaudari ’yan matan ne a lokuta daban-daban, a lokacin da yayi musu fyaden kan ’yan matan masu shekaru 16 da 13.
Bayan samun korafin, kwamandan, Eagle-Net ya yi cikakken bayani kan masu binciken don yin bincike kan lamarin.Jami’in binciken ya zage damtse wajen ganin an kama wanda ake zargin.sai dai kuma “Da aka yiwa wanda ake zargin tambayoyi ya amsa laifinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An gudanar da gwajin lafiya kan wadanda abin ya shafa.sai dai “A halin yanzu wanda ake zargin yana tsare kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu idan an kammala bincike,” inji shi.