By Abbas Yakubu Yaura
Wasu mutane biyu sun tsallake rijiya da baya inda suka kubuta daga cikin wani jirgin daya fado bayan daya kutsa cikin ruwa a bakin tekun City Beach dake Perth, mai tazarar kilomita 10 daga CBD na kasar Australia.
‘Yan sanda sun mayar da martani ga rahoton wani karamin jirgin sama daya afka cikin ruwan jim kadan bayan karfe 3:30 na yammacin ranar Asabar, agogon kasar.
Insfekta Vic Hussey ya shaida wa manema labarai cewa an kwashe kimanin mintuna 20 zuwa 30 ne a sararin samaniya bayan da jirgin ya tashi daga filin jirgin sama na Jandakot, lokacin da matukin jirgin ya bada rahoton wata samuwar wata matsala ta inji.
“Na tashi zuwa arewa ƙetaren bakin teku. Sai kawai yace da ni yana neman wurin da zai sauka, kuma wurin daya fi aminci shi ne teku, a nan ne ya sauka,” in ji Insfekta Hussey.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘Yan kallo sun yi iyo suka fito domin taimakawa matukin jirgin da fasinjansa, wadanda dukkansu suka yi nasarar fita daga cikin jirgin ta tagoginsa, suka nufi gabar teku, kimanin ta zarar mita 20.
Kazalika Insfekta Hussey yace mutanen biyu, abin mamaki, “duk sun yi sa’a”, kuma bayan da suka kubuta ne suka ce “ya kamata suje su sayi tikitin caca”.
“Suna lafiya, Babu rauni. Duk suyi sa’ar kubuta. Yau rana ce mai albarka a gare su,” inji shi.
Sai dai a martanin da jami’an bayar da agajin gaggawa suka bayar sun hada da ‘yan sanda da dama da kuma ‘yan sandan cikin ruwa da wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sandan Air Wing wajen bada agaji.