Akalla mutane 5,000 ne aka kashe a hare-hare 200 da aka kai jihar Benue biyo bayan yaduwar da makamai suka yi a kauyaku cikin shekaru 11 da suka gabata. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Gwamna Samuel Ortom ya fitar da wannan adadi ne a ranar Larabar, yayin da ake rattaba hannu a kan kudirin dokar samar da zaman lafiya da sulhu a jihar ta Benue.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje Ya Maida Gidan Mataima Sule, Gidan Tarihi
“Hanyar zuwa wannan taron mai cike da tarihi ta kasance ta hanyar ƙalubalen da ake da su. Kamar yadda kuka sani, sama da mutanenmu 5,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da ba a san ko su waye ba suka kai, ta hanyar cin zarafin makiyaya tsakanin 2011 zuwa Yuni 2022.
“Abin ban tsoro ne ganin cewa jihar Benue ta sha fama da hare-hare sama da 200 a cikin wannan lokaci tare da lalata dukiya ta sama da Naira biliyan 500.
“Don haka, lokacin da muka yi kuka, saboda mutanenmu da ƙasarmu ana kai musu hare-hare. Kuma kamar yadda muka yi kamun kafa ta hanyar rashin daukar makami a kan maharan, don haka bazamu iya bari lamarin ya cigaba da gudana ba ” inji gwamnan.
Ortom ya ci gaba da cewa, abin takaici, kalubalen tsaro da ya haifar da matsalar da ake fama da shi a yanzu a jihar, yanzu haka lamarin ya jefa Benue cikin matsalar karancin abinci, haifar da jahilai kamar yadda wasu yara suka kasance a sansanonin ‘yan gudun hijirar (IDP) sama da shekaru bakwai ba tare da makaranta ba; matsalar rashin lafiyar kwakwalwa da ke tasowa saboda raunin da ba a warkewa, da sauransu.
Tun da farko, kodinetan Majalisar Dinkin Duniya da ayyukan jin kai, Matthias Schmale, ya yabawa masu goyon bayan matakan zaman lafiya, tattaunawa, sasantawa don kawo karshen tashin hankali da kuma kare rayuka a kowane yanayi a fadin Najeriya.
Schmale ya ce, “Tare da kimanin kabilu 374 da kuma harsuna kusan 552 da ke magana da mutane sama da miliyan 206, babu iyaka ga abin da Najeriya za ta iya cimma idan ta sanya hankalinta wajen shigar da ‘yan kasa baki daya shirin zaman lafiya, ta yin amfani da ilimi, al’adu, da tallafin gwamnati. .”
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: ASUU Na Kokarin Shigar Da Kara, Kan Hukuncin Da Aka Yanke Mata
Kungiyar malaman jami’o’i ta sha alwashin daukaka kara kan umarnin kotun kula da da’ai Ma’aikata ta kasa, inda ta umurci malaman da su koma bakin aikin au cikin gaggawa.
Kungiyar ta ce ta fara hada lauyoyinta karkashin jagorancin fitaccen dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, babban lauyan Najeriya, domin shigar da kara.