Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta sayi gidan marigayi Dan Masanin Kano, Ambasada Yusuf Maitama Sule, kuma za ta mayar da shi Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya da Shugabanci na gari da kuma gidan tarihi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: ASUU Na Kokarin Shigar Da Kara, Kan Hukuncin Da Aka Yanke Mata
Ya kuma ce tuni aka fara aikin gine-gine a gidan marigayin, wanda kuma tsohon Jakadan Najeriya ne a Majalisar Dinkin Duniya, da kuma gidan Gwamnatin Birtaniya da aka fi sani da British Council da ke kan hanyar gidan Sarki a birnin Kano.
Kwamishinan ya kuma ce an ware Naira miliyan 621 domin aikin wanda aka kasa shi gida biyu, inda kashin farko zai fara da gidan tarihi da kuma na cibiyar, yayin da za a fara ginin da na gidan tarihin.
Malam Garba ya ce gwamnati ta yanke shawarar fara aikin ne domin ta adana tarihi saboda muhimmancinsu ga al’ada da tarihin mutanen jihar, domin amfanin manyan gobe da kuma yawon bude ido.
Daga cikin abubuwan da ake sa ran cibiyar za ta rika gudanarwa sun hada da bayar da horo, adanawa da zamanantar da al’adun jihar Kano da kuma samar da hadin gwiwa da sauran cibiyoyin ilimi da ke ciki da wajen Najeriya a fannin bincike.
A WANI LABARIN KUMA: Yan sanda Sun Kubutar Da Wani Mutum Daga Hannun Yan bindiga, Sun Kwato Harsasai
Jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda mai kula yankin Agbarho da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta, sun ceto wani da aka yi garkuwa da su tare da kwato harsashi guda hamsin (50) daga wurin da lamarin ya faru.
An kubutar da wanda akakaman ne biyo bayan bayanin da jami’in ‘yan sanda na yankin DPO ya samu cewa wasu ‘yan bindiga sun kasance a gidan mamacin da ke kan titin jirgin kasa na titin Agbarho kuma sun yi garkuwa da su.