Wani dan ta’adda ya rasa ransa yayin da jami’an tsaro suka dakile wani hari da Yan bindiga suka yi yunkurin kai wa a Hayin Gada da ke unguwar Shika na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki yankin ne a daren Juma’a.
Maharan da suka zo Basu da yawa, sun zo ne da misalin karfe 11 na daren Juma’a sun gamu da fushin jami’an tsaro da tuni suka kafa sansanj a yankin.
Yan bindiga sun ci gaba da addabar karamar hukumar Giwa a ‘yan kwanakin nan.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta gano cewa ‘yan ta’adda sun tsere zuwa yankin yayin da ake ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a jihohin Zamfara da Katsina.
Unguwar Shika kuma ita ce wurin zama na Asibitin Koyarwa na jami’ar ABU da Cibiyar Binciken Kiwon Dabbobi ta Kasa, inda ma’aikatan wannan cibiya da ABU Zariya ke rayuwa a wajan.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa daya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa ne a yayin wani artabu da jami’an tsaro a lokacin da yake kokarin guduwa.
Sai dai kuma jami’an tsaron sun yi nasarar ceto ma’aikatan Cibiyar Binciken Kiwon Dabbobi ta Kasa, NAPRI dake garin na Shika, Mai suna Mr.Katung da ‘ya’yansa guda biyu daga hannun Yan bindigan.