Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shugaban karamar hukumar Kuje mai ci Abdullahi Suleman Sabo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022.
Sabo ya doke sauran ‘yan takara biyar a dukkan shiyya 10 na yankin.
Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC mai kula da zaben kananan hukumomin Kuje, Sule Magaji ne ya sanar da sakamakon karshe a ofishin hukumar a safiyar yau Lahadi.
Ya bayyana cewa shugaban da ke kan karagar mulki ya samu jimillar kuri’u 13,301 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Sarki Hamidu Gaube na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 7,694.
Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a yankin, Loveday Ajo, ya samu kuri’u 79.
A wani labarin Kuma na daban.
Akalla mutane uku ne suka mutu tare da ceto wasu mutane biyu da ransu a karkashin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Yaba da ke jihar Legas ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa ginin bene mai hawa uku da ake ci gaba da yi ya ruguje inda ya rufta kan wani ginin da ke gefensa a Akanbi Crescent a unguwar Yaba a jihar Legas.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas da wasu masu aikin ceton da suka isa wurin, an ce sun isa wurin ne sa’o’i guda bayan rugujewar domin fara aikin ceto.
Darakta Janar na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce dukkan gawarwakin da aka gano manyan maza ne, kuma ana ci gaba da kokarin ceton rayuka.
Oke-Osanyintolu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nosa Okunbor, ya fitar mai take, ‘Rahoton Halin da ake ciki kan Rugujewar Gine-gine a Titin Akanbi Kusa da Babban Kofar Unilag’.
Ya bayyana cewa jami’an agajin gaggawar sun kwaso gawarwakin tare da ceto wasu da ke raye sakamakon tura manyan na’urorin hukumar cikin gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa, “An sabunta: An kuma gano wani babba namiji da ya mutu a karkashin baraguzan ginin.
“Jimlar ƙidaya har zuwa karfe 23:00 na safe. An ceto mutane 2 manya maza a raye inda aka samu Matattu 3 manya maza.”
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto ga sauran wadanda abin ya shafa.