Rahotanni na nuna cewa, Wasu yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, sun hallaka yan garin Modekeke dake jihar Osun, wadanda aka bayyana cewa, suna kan hanyar zuwa gonar su ne dake kyauyen Toro a sanyin safiyar yau juma’a.
Wani jagoran garin Modakeke Mr Femi Eluyinka ne ya tabbatar wa da mane ma labarai hakan, inda ya ce, wasu mutanan yankin da jami’an yan sanda sun kwashe gawar-wakin mamatan.
Eluyinka ya kara da cewa, al’umar garin na cikin firgici sakamakon lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC ta Garkame wani Asibitin Sanata Kwankwaso
Ya ce” Jami’an yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru, bayan da hankulan jama’a ke dada tashi, mutane biyar din dukkannin su yan garin Modakeke ne, Kuma an kashe sune a hanyar Toro lokacin da su ke kan hanyar zuwa gona.” Inji shi.
Ko da aka tuntumi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Yemisi Opalola, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Inda bayyana cewa, ” Munsami labarin cewa, an kashe mutune biyar, kuma Kwamishinan yan sanda na jihar Osun, ya bada umarnin tura jami’an yan sanda yanki, domin wanzar da doka da oda” inji shi.