Wasu makiyaya da ba a san adadinsu ba a daren ranar Juma’a, sun kai farmaki kauyen Igbooro, Oja-Odan a karamar hukumar Yewa ta Arewa da ke jihar Ogun, inda suka kshe mutane 3 tare da jikkata wasu biyu.
Makiyayan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, sun kai hari kauyen ne da kusa da Eggua, a Oja-Odan, da misalin karfe 11 na daren ranar Juma’a, inda suka rinka harbin kan mai uwa da wabi, tare da kona gidaje uku da rumbunan ajiyar abinci a kauyen.
Rahotanni sun bayyana cewa, daga cikin mutane 3 da aka kashe, akwai wata mata da karamin yaronta, yayin da wasu mutane 2 ke cikin mawuyacin hali bayan harbinsu da makiyayan suka yi.
Haka zalika an gano cewa mutane da yawa, ciki har da kananan yara, sun samu raunuka daban daban.
Wannan harin na zuwa ne kasa da awanni 24 da aka kashe wasu mutane 5 a Owode Ketu, duk a cikin jihar ta Ogun.
Da ya ke tabbatar da kai wannan hari, Sarkin garin Igbooro, Abidemi Akorede, ya ce ya kirga gawarwakin mutane 3, a lokacin da ya ke zantawa da wakilin jaridar Premium Times a safiyar ranar Asabar.
Akorede ya ce mutane biyu, mace da namiji, sun samu munanan raunuka daga harbin da makiyayan suka yi masu, an kuma garzaya da su asibiti domin ceto rayukansu.