A na fargabar cewa an kashe mutane uku a ranar Lahadi a Amawbia da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.
An ce daya daga cikin wadanda suka mutu yana cikin jami’an tsaron shugaban jam’iyyar APGA na kasa, Cif Victor Oye.
Wata majiya a yankin ta ce kisan na iya kasancewa na da nasaba da yakin kungiyar asiri da ya yi sanadin salwantar rayuka da dama a kananan hukumomin Awka ta Arewa da ta Kudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ba zai iya magana kan adadin mutanen da aka kashe ba.
Ya ce an yi harbe-harbe a Amawabia kuma mutane biyu ne kawai aka harbe, ya kara da cewa “ban tabbata ko sun mutu ba”.