By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kogi ta dawo da wasu yara 34 da aka yi safararsu zuwa jihar Filato.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma, Hajiya Fatima Kabir Buba, ce ta bayyana hakan a ranar Lahadin data gabata yayin ganawar ta da manema labarai a Lokoja.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a ranar Alhamis din data gabata ta kama wasu motoci biyu na kasuwanci, Toyota Sienna da wata motar bas Mazda mai lamba Lagos LND-124-FV da kuma Oyo BDJ-683-YK a kan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja, sun yi jigilar kananan yara ne daga jihar Ogun zuwa jihar Filato da ake zargin kungiyar masu safarar mutane ce.
A yayin da ake yi musu tambayoyi, direbobin bas din sun ce wata mata mai suna Mama Blessing wadda aka fi sani da Martina ta mika musu yaran a Ijebu-Ode domin a kai su Abuja, inda suka ce da zarar sun isa babban birnin tarayya, matar za ta kira wayar wani direban bas, wanda zai kai su Riyom ta jihar Filato.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Buba tace yaran da aka dawo dasu basu wuce shekara tara zuwa 19 ba.
Sannan ta ci gaba da cewa, “Bayan tattaunawa da bincike da ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a a jihar Kogi ta yi, mun yi nufin fahimtar cewa duk yaran da aka yi safarar su ‘yan jihar Filato ne. Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin inda aka mayar da yaran jiharsu aka mika su ga ma’aikatar harkokin mata don haduwa da iyayensu.
“A nan yana da mahimmanci a bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi a karkashin gwamnan mu, Alhaji Yahaya Bello, za ta ci gaba da kare yara tare da tabbatar da cewa miyagu ba su da wurin hayayyafa a jiharmu.
Gwamnatinmu za ta bi wannan lamari tare da tabbatar da an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.”
A cewarta, tuni ma’aikatar ta rubutawa ma’aikatar harkokin mata ta jihar Ogun domin gano wanda ake zargi da safarar mutane, inda ta kara da cewa Daraktan ayyuka na hukumar hana fataucin mutane ta kasa Mista Daniel Atokolo na gudanar da bincike domin gano bakin zaren. duk membobin kungiyar dake da hannu a cikin haramtacciyar kasuwancin.