Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya ce jam’iyyar PDP za ta rika amincewa da Yarjejeniya a tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mayar da dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima domin amincewa da majalisar dokokin kasar, yana mai cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ba ta da ikon sanya ido kan zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa 18 kai tsaye.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Ortom, ya ce jam’iyyar PDP za ta yi amfani da zabin yarjejeniya a dukkan matakai, ciki har da dan takarar shugaban kasa wajen zabar masu rike da madafun iko a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa kawo yanzu sama da ‘yan kasa 1700 da jami’an tsaro 100 ne aka kashe a rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito Orton na cewa “A shekarar 2023, za mu yi amfani da zabin yarjejeniya wajen fitar da dukkan ‘yan takara da kuma inda ba za mu iya cimma matsaya ba kamar yadda muka yi a zaben ‘yan kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da kuma inda ba za mu iya kaiwa ga gaci ba, sai mu yi yarjejeniya a zaben”.