Wata farfesa a birnin Minnesota na ƙasar Amurka, ta rasa aikinta bayan ta nunawa ɗalibai zanen hoton Annabi Muhammad (SAW) a cikin aji.
Farfesar mai suna Erika López Prater, mai shekara 42, an koreta daga aiki a jami’ar Hamline a Saint Paul, bisa nuna zanen hoton wanda yake na ƙarni goma sha huɗu ne. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KARANTA KUMA: Dangote ya fara 2023 da ƙafar dama, ya kafa wani babban tarihi
Jami’ar ta Hamline ta kori Farfesar ne saboda rashin mutunta ɗalibai musulmai inda ta fifita ƴancin koyarwa fiye da mutuncin addinin su.
A wata takarda da shugabar makarantar, Fayneese Miller ta fitar, ta nemi yafiya akan lamarin sannan tace rashin ɓatawa ɗalibai musulmai na makarantar abu ne mai matuƙar muhimmanci.
‘Ba manufar mu bace mu ɗora laifi, saidai niyyar manufar mu itace mu nunar da cewa lamarin da ya faru a aji inda aka nuna wani hoton da bai halarta musulmai su kalla ba, an sanya shi sannan aka bar shi na wasu ƴan mintuna. Mutunta ɗalibai musulmai dake a wannan ajin yakamata ace yafi ƴancin koyarwa. Inji Miller.
Wata musulmar ɗalibai mai suna Aram Wedatalla, itace ta shigar da ƙorafi kan lamarin inda tace anyi mata rufa ido.
FG Za Ta Ci Gaba Da Shari’ar Wadanda Ake Zargin ‘Yan Boko Haram Ne
Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen ci gaba da kashi na biyu na gurfanar da wadanda ake zargi da Boko Haram a wani sansanin soji da ke Kainji a jihar Neja.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma babbar sakataren ma’aikatar shari’a na tarayya, Beatrice Jedy-Agba, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da take zantawa da manema labarai a Abuja.
Agba ya ce an ci gaba da tsare-tsare da kuma shirye-shirye masu yawa don sake dawo da ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.