Wanda yafi kowa arziƙi a Najeriya, Aliko Dangote, ya fara shekarar 2023 da ƙafar dama inda ya koma mutum na 78 cikin jerin masu arziƙin duniya.
Hakan na nufin ya ƙara matsawa sama da matsayi 22 daga na matsayi na 100 wanda yake a shekarar 2022 cikin jerin na masu arziƙin duniya wanda Bloomberg ke fitarwa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KARANTA KUMA: Matar shugaban hukumar DSS ta bayar da umurnin cafke ɗan takarar gwamnan Kano na NNPP
Duk da wannan matsawa sama da yayi, arziƙin Dangote ya ragu da $4000m (N182bn) a cewar Bloomberg.
A ranar Lahadi, 8 ga watan Janairun 2023, arziƙin Dangote yana a $18.7bn saɓanin $19.1bn wanda ya fara da shi a watan Janairun 2022.
Matsawa sama dDangote yayi a cikin jerin masu arziƙin na duniya ya samu asali saboda karayar arziƙi da wasu attajiran duniya suka samu musamman ƴan ƙasar Rasha.
A cikin ƴan kwanakin nan an rahoto cewa attajiran duniya sun yi asarar da ta kai ta $1.4trna shekarar 2022.
Jerin sunayen attajirai biyar mafiya kuɗi a farkon shekarar 2023
- Bernard Arnault
Elon Musk
Gautam Adani
Warren Buffett
Jeff Bezos
Aliko Dangote shine kaɗai ɗan Najeriyan da sunan shi ya fita a cikin jerin masu arziƙin duniya na Bloomberg.
Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Jirgin Kasan Edo
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi Allah wadai da harin jirgin ƙasan jihar Edo
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da harin jirgin kasa na Edo, yana mai cewa “tunawa ne a kan bukatar gaggawar sake fasalin tsarin tsaron mu domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.”
Ku tuna cewa sama da fasinjoji 30 da ma’aikatan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) ne ake kyautata zaton an sace sakamakon farmakin da masu garkuwa suka kai a daren ranar Asabar a tashar jirgin kasa ta Igueben da ke jihar Edo.