Ƴan bindiga a safuyar ranar Juma’a, 20 ga watan Janairun 2023, sun sace ɗaliban wata makarantar firamare a jihar Nasarawa.
Ƴan bindigan sun sace yaran ne a makarantar firamare ta Alwaza, a ƙauyen Alwaza cikin ƙaramar hukumar Doma a jihar Nasarawa, inda suka yi awon gaba ɗa ɗalibai da dama. Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Ƙilu ta janyo bau: Kotu ta umurci wata budurwa biyan maƙudan kuɗaɗe bayan ta cinye kuɗin saurayi
Dimokuradiyya ta samo daga majiyarmu cewa ƴan bindiga waɗanda suka sace ɗalibai da dama waɗanda ba a san adadin su ba, sun yiwa makarantar ƙawanya ne lokacin da yaran ke zuwa makaranta.
Har ya zuwa yanzu ba a san inda yaran da waɗanda suka sace su ke ba.
Kakakin hukumar ƴan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
A cewar rundunan ƴan sandan jihar, an tura tawagar ƴan sanda, sojoji da ƴan sakai domin bin sawun ƴan bindigan waɗanda suka zo a kan babura.
Kwamandan Amotekun Ya Yi Murabus daga Matsayin Sa
A wani labarin na daban kuma, babban kwamandan rundunar tsaro ta jihohin Kudu maso Yamma wato Amotekun, yayi murabus daga muƙamin sa.
Babban Darakta Janar kuma Kwamandan rundunar Amotekun ta Osun, Amitolu Shittu, ya yi murabus daga mukaminsa.
Sanarwar tana kunshe ta cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sa na Facebook ranar Juma’a, ya ce tun a lokacin ya mika takardar murabus dinsa ga ofishin sakataren gwamnatin jihar.