Hukumar Yansanda ta tabbatar da kashe wani Jami’in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA, a jihar Nasarawa.
Yansanda reshen Jihar Nasarawar sun ce Jami’in mai suna Mista Dennis Onoja, an tsinci gawarsa a dakin sa Jina-Jina.
Jami’in hulda da Jamaa na hukumar Yan sandan Jihar ASP Usman Samaila, ya tabbatarwa da Manema labaru aukuwar hakan a ranar Alhamis a Lafiya.
ASP Samaila, yace batun ya faru a daren ranar Laraba, a Tudun-Kauri a cikin garin Lafia babban birnin lafiya.
Yace,makoncin sa ne ya tafi dakin sa don ya saka chajin batirin sa saboda ba shi da Wuta shi kuma ya kunna Na’urar Janereto, bayan makonci ya dunga bubbuga kofar dakin nashi yaji shiru sai ya leka ta Hundo sai ya tsinkaye shi Jina jina, take ya sanar da hukumar Yan sanda.
Ko da ake bude kafar sai aka same shi duk an sassare shi da Adda, gashi kwance Jina Jina, kuma da Alama an dan taba dambe Tsakar dakin.
Zuwa yanzu baa Iya gane wadanda suka aikata danye aikin ba amma hukumar Yansanda tace zata hada Hannu da hukumar NDLEA wajen ganin sun gano wadanda suka aikata hakan.