A ranar Litinin ne aka kwantar da tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda a asibiti cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Wata sanarwa daga ofishin Tsohon Shugaban Kasar ta ce an kwantar da Mista Kaunda ne a asibitin sojoji dake birnin Lusaka na kasar.
To sai dai hr kawi yanzu da muke haɗa muku wannan rahoto, babu wani karin haske dangane da halin lafiyar nashi.
Mista Kaunda ya mulki Zambia na tsawon shekara 27 bayan da kasar ta samu yancin kai daga turawan mulkin Birtaniya a shekarar 1964.
Yanzu haka dai an ruwaito cewa tsohon Shugaban Kasar ya mika bukatarsa ga jama’a da su taimaka masa da addu’a, duk da cewa likitoci na iya bakin kokarin su na ganin sun ceto rayuwarsa.