By Ishaq Dabai
A kalla an rufe layikan sadarwa a kananan hukumomin 13 dake jihar inda iya jami’an tsaro ne kadai keda ikon yin amfani da shi domin gudanar da aikinsu biyo bayan aikace aikacen ‘yan bindiga a Arewa maso yamma.
Kananan hukumomin da abin yashafa sun hadar da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da kuma karamar hukumar Kurfi bayanda ‘yan bindiga suka boye a dajin Ruggu.
Sauran sun hadar da Funtua, Bakori, da kuma Malumfashi.
Wannan yana zuwa ne ‘yan kwanaki kadan da hukumar sadarwa ta kasa NCC ta musanta cewa ta rufe kafofin sadarwa na jihar Katsina.
Kafin wannan lokaci dai hukumar ta NCC ta rufe kafofin sadarwa na jihar Zamfara dan baiwa jami’an tsaro damar jin aikin su.