Bayanai daga kasar Indiya na nuni da cewa; an sallami shahararren ɗan wasan fim ɗin Bollywood, Amitabh Bachchan daga asibiti bayan gwajin da aka yi masa wanda ya yi nuni da cewa; ba shi dauke da cutar korona din a yanzu.
A wani sako da Bachchan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya tabbatar da cewa ya warke daga cutar, inda yanzu ya koma gida comin killace kansa.
Aminta Bachchan mai shekaru 77 a duniya, ya yi fina-finai 200 cikin shekaru 50.
Tun a ranar 11 ga watan Yuli gwaji ya tabbatar da Mista Bachchan ya kamu da cutar.