An samu karuwar mutane 71 da suka kamu da cutar Covid-19 a Najeriya
Hukumar dake yaki da cututtuka ta sanar da kamuwar mutane 71 a Najeriya a yau, wanda kawo yanzu a sami mutane 167,803 da suka kamu da cutar.
Hukumar ta sanar da hakane a shafinta na kafar sada zumunta, masu tattara bayanai sun ce an samu karuwar mutane 40 kan na niya.
KARANTA:-Kungiyar Crystal Palace ta dauki Vieira a matsayin sabon mai horas da Yan wasa
Hukumar dai tace babu wanda ya rasa ransa kan wannan cutar a kasar, cikin Yan kwanakwanannan.
An tabbatar da kamuwar mutane 167,803, inda aka sallami 164,378 tun farkon bullowar cutar, sa’annan mutane 2,121 suka mutu a gaba daya jahohi 36 na Najeriya.
Hukumar tace wadanda suka kamu da cutar a jiya sun fito daga jahohi hudu ne kamar haka, Lagos 63, Oyo 4, Ogun 3 and Kano 1.
Hukumar ta kara jawo hankalin mutane dasu cigaba da kiyaye dokokin cutar don gudun yaduwarta cikin Al’umma.
Tace mutane su cigaba da yin amfani da Facemask, wanke hannu da bada tazara.
Comments 1