An sami sabbin masu kamuwa da cutar kyandar biri a Najeriya mutane 100 da ake zargin sun kamu da cutar, kamar yadda Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Kasa (NCDC) ta sanar a ranar Lahadin nan.
Hukumar da ke da alhakin auna tasirin cututtuka masu yaduwa ta kuma bayyana ta hanyar wani rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, an auna jihohi 21 na tarayyar kasar nan.
Jihohin sun hada da Legas (17), Abia (16), Imo (14), Delta (7), Ondo (7), Bayelsa (5), Gombe (5), Ribas (4), Benue (3), Ebonyi ( 3), Edo (3), Plateau (3).
Karanta kuma: Cutar Kyandar Biri Ta Kama Sama Da Mutane 1000 A Nahiyar Afrika
Birnin tarayya FCT, Katsina, Osun, da Taraba, suna da jimillar (2) yayin da Anambra, Enugu Kano, da Oyo duk sun sami mutum guda.
Ya kuma bayyana cewa daga 1 ga Janairu zuwa 28 ga watan Agusta, 2022, Najeriya ta samu mutane 704 da ake zargi da kamuwa da cutar, yayin da 277 aka tabbatar sun kamu da cutar (maza 186, mata 91) daga jihohi talatin (30) – Legas (49), Ondo (22), Bayelsa (19), Rivers (18), Edo (16), Adamawa (15), Abia (15), Delta (14), FCT (11), Imo (11), Anambra (10), Nasarawa (9), Ogun (7). ), Plateau (6), Taraba (5), Kwara (5), Kano (5), Gombe (5), Ebonyi (5), Oyo (5), Katsina (5), Cross River (4), Benue ( 4), Borno (3), Kogi (3), Akwa Ibom (2), Niger (1), Bauchi (1), Osun (1) sai Kaduna na da (1).”
“An samu rahoton mutuwar mutane shida (6) daga jihohi 6 a shekarar 2022 – Delta (1), Legas (1), Ondo (1) da Akwa Ibom (1), Kogi (1) da Taraba (1),” in ji sanarwar.
Sai dai tun bayan sake bullar cutar a shekarar 2017, jihohi biyar (5) (Kebbi, Sokoto, Zamfara, Jigawa, Yobe) ba a tabbatar da sun kamu da cutar ba, yayin da jihohi biyu (2) (Jigawa da Yobe) basu bayar da rahoton wani da ake zargi da kamuwa ba. A shekarar 2022, Jihohi Bakwai (7) har yanzu ba a tabbatar da kamuwa da cutar ba (Enugu, Ekiti, Kebbi, Sokoto, Zamfara.
An samu rahoton bullar cutar guda 1216 daga jihohi 35 na kasar tun bayan sake bullar ta a watan Satumban 2017. Daga cikin wadannan, 503 (41%) sun tabbatar da kamuwa da cutar yayin da Maza ke wakiltar kashi 66% (334) daga jihohi 32.
A wani labarin kuma: Macron Ya Bukaci Putin Ya Janye Makamai Daga Tashar Nukiliyar Ukraine
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Lahadin nan da ya janye makaman Rasha daga tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia yayin da Putin ya yi gargadin cewa “mummunan sakamako” na abin da ya ce harin da Ukraine ta kai a cibiyar.
A cewar Elysee, Macron ya gaya wa shugaban na Rasha a cikin wani kira da ya yi cewa “mamayen Rasha ya haifar da hadarruruka.