An sanya kulob ɗin Everton na ƙasar Ingila wanda ke buga gasar cin kofin Premier League a kasuwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta samo daga shafin Linda Ikeji cewa mamallakin kulob ɗin mai suna Farhad Moshiri, mai shekara 67 a duniya shine ya saka kulob ɗin a kasuwa.
Moshiri wanda ya kwashe watanni yana neman masu zuba jari da su zo su saka a kulob ɗin, kafin ya yanke shawarar siyar da kulob ɗin yana neman kusan £500m, kafin ya siyar da kulob ɗin.
KU KARANTA KUMA: Amarya ta fasa aurenta ana gobe biki bayan ta gano wani ɓoyayyen sirri
An yi amanna cewa Moshiri yana son ya dawo da maƙudan kuɗaɗen da kashe wajen gina sabon filin wasan kulob ɗin, wanda aka gina a birnin Liverpool.
Masu siya da dama sun nuna aniyar su ta siyan kulob ɗin, inda wasu da dama akayi hasashen za su siya kulob tunda farkon wannan kakar wasannin.
Everton yanzu na can a ƙasan teburi insa suke a matsayi na 19 bayan sun samu maki 15 kawai daga cikin wasanni 20 na wannan kakar.
Barazanar komawa gasar ƙasa da Premier League ta sanya kulob ɗin ya faɗa cikin dambarwa, inda har ya zuwa yanzu ba su da mai horar da ƴan wasa bayan sun sallami Frank Lampard.
Babban kamfanin Deloitte na ƙasar Amurka shine aka baiwa alhakim siyar da kulob ɗin.
Moshiri ya siya kaso 49.9 a kulob ɗin ne a shekarar 2016 kan kuɗi £200m.
Messi Na Shirin Watsawa PSG Ƙasa a Ido, Akwai Yiwuwar Zai Koma Barcelona
A wani labarin na daban kuma Lionel Messi yayi watsi da tayin sabunta kwantiraginsa da PSG tayi masa, akwai yiwuwar ya bar kulob ɗin.
Dukkanin alamu sun nuna cewa Lionel Messi zai tsawaita kwantiragin sa da Paris Saint Germain, bayan kakar 2023 dake tafe.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa ɗan wasan baya muradin cigaba da zama a kulob ɗin.
Lionel Messi ya bar Barcelona a shekarar 2021, sannan ya koma PSG a kyauta inda ya haɗu da tsohon abokin sa Neymar.