Kamfanin raba wuta na Nijeriya wato TCN ya bayyana cewa tuni suka shawo kan matsalar da ta shafi matattarar wutar lantarki ta kasa da ya auku a ranar Alhamis.
Matattarar wutar ya auku ne a daidai lokacin da take kokarin dawo hayyacinta daga matsalar da ta samu a kwanakin baya.
Ndidi Mbah, Manajar hulda da jama’a na TCN din ita ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Juma’a.
Mbah ta ce tuni suka cimma nasarar shawo matsalar da ta addabi matattarar wutar ta kasa.
Ta ce wurin ya fuskanci matsala ne a ranar Alhamis da misalinn karfe 12.34 na rana.
Ta ce duk da matsalar da ya samu, amma yana bai wa al’ummar Fatakwal, Aba, Omoku, Yenegoa, Afam, da sauran su wutar lantarki ta tasoshin wuta na Afam IV, Rivers Independent Power Plant da kuma Omoku Power Stations.
Mbah ta ce an fara cimma nasarar shawo matsalar ne da misalin karfe 10 na daren Alhamis. Wanda ta ce tuni wasu wuraren suka fara samun wutar. Sai dai ta ce a ranar Juma’a da misalin karfe 2:19 na dare aka shawo kan matsalar baki daya.